Sidibé ya bayyana wa wakilan kamfanin dillancin labaru na Xinhua a wannan rana cewa, shugabannin kasar Sin suna dora muhimmanci sosai kan rigakafi da yaki da cutar ta kanjamau, da kokarin kawar da nuna bambanci ga mutanen da suka kamu da cutar, tare da daukar matakai masu inganci.
Hakazalika kuma, Sidibé ya yabawa kokarin kasar Sin na dakile yaduwar cutar daga mahaifiya zuwa ga jaririnta. Ya ce, tun daga shekarar 2014, ba a gano wani jariri a birnin Beijing da ya kamu da cutar ba bayan da aka haife shi. (Zainab)