in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta cimma nasarar hana yaduwar cutar AIDS a tsakanin mahaifiya da jaririn ta
2016-03-19 12:30:29 cri

Daraktan hukumar kula da harkokin da suka shafi cutar AIDS ta MDD (UNAIDS) Michel Sidibe, ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, kasar Sin na cikin kasashen da suka fi nuna kwarewa, a fannin kandagarkin yaduwar cutar AIDS, inda ake sa ran za ta cimma nasarar dakile yaduwar cutar a tsakanin mahaifiya zuwa jaririn ta nan da dan lokaci.

A jiyan ne dai Mr Sidibe ya sa hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa, da shugaban kamfanin dillancin labaru na Xinhua Cai Mingzhao a birnin Geneva, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin karfafa hadin gwiwa, a fannin yada bayanai ta kafofin watsa labaru, domin ba da gudummawa ga yakin da ake yi da yaduwar cutar AIDS.

Bugu da kari, Michel Sidibe, ya ce kowa ya san alkawarin da shugabannin kasar Sin suka yi a fannin kandagarkin cutar AIDS, da kuma kyakkyawan sakamakon da aka samu a wannan fanni. A cewar sa kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannonin zakulo sabbin hanyoyin kandagarki, da warkar da cutar AIDS. Don haka ya yi imanin cewa, kasar za ta zama kawa mafi muhimmanci ga hukumar UNAIDS a shekaru 15 masu zuwa, kana za ta kara ba da gudummawa wajen yaki da cutar.

A nasa bangare, Cai Mingzhao, ya bayyana cewa tun daga shekarar 2011 da bangarori biyu suka kulla yarjejeniya, sun gudanar da hadin gwiwa mai inganci, tare da karfafa hadin gwiwarsu yadda ya kamata. Kaza lika yana da imanin cewa bangarorin biyu, za su yi kokarin ba da gudummawa ga aikin kawo karshen cutar AIDS kafin shekarar 2030, ta hanyar yin amfani da wannan zarafi. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China