in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ayyana kawo karshen yaduwar cutar AIDS kafin shekarar 2030
2016-06-09 12:57:03 cri

A jiya Laraba kasashe membobin MDD sun ayyana kawo karshen cutar AIDS a siyasance, inda suka yi alkawarin yin aiki tare don hana yaduwar cutar, da cimma jerin buruka da aka tsara kafin shekarar 2020, haka kuma, za su yi kokarin cimma burin kawo karshen yaduwar cutar AIDS kafin shekarar 2030.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, kasashen duniya sun samu gagarumar nasara a fannin yaki da yaduwar cutar AIDS, amma duk da haka ana bukatar karin lokaci don kawar da ita. Ya yi kira ga hukumomin lafiya na duniya da kasashe membobin MDD da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kwamitin sulhu na MDD da su kara dora muhimmanci kan batun cutar AIDS, domin ci gaba da inganta hadin gwiwar kasashe daban daban wajen tinkarar cutar, sa'an nan a daina nuna bambanci ga mutanen dake fama da wannan cuta a lokacin da ake ba su jinya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China