Mataimakin babban sakataren MDD, kana darektan gudanarwa na hukumar yaki da cutar AIDS na MDD Michel Sidibe, ya bayyana a gun taron cewa, an rage yawan kudaden da ake zubawa don yaki da cutar a daidai lokacin da aka fi bukatarsu.
A cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasashe masu sukuni, da wasu kungiyoyi na duniya sun rage yawan kudade da suke zubawa don yin nazari da shawo kan cutar AIDS. An ba da labarin cewa, a cikin shekaru 15 da suka wuce, jimillar kudin yaki da cutar AIDS ya rage dala miliyan daya ne kachal a kowace shekara. A sabili da haka, mahalarta taron suna ganin cewa, ko da yake an sami babban cigaba wajen shawo kan cutar, amma har yanzu ba a kammala aikin ba. Kamata ya yi kasashe masu sukuni su kara zuba kudade domin taimakawa kasashe masu tasowa wajen ci gaba da yin gwagwarmaya da cutar AIDS. (Fatima)