Sidibe ya bayyanawa 'yan jarida cewa, shugabannin kasar Sin sun dora muhimmanci tare da shiga ayyukan yaki da cutar AIDS, wadda wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga dukkan al'ummar kasar shiga aikin yaki da cutar. Sin ta samu nasarori kan magance da yaki da cutar AIDS, Sidibe ya ce, yana fatan Sin za ta more fasahohinta na yaki da cututtuka masu yaduwa tare da kasa da kasa.
A nasa jawabin Direktan gudanarwa na asusun yaki da cutar AIDS, tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro Mark Dybul ya bayyanawa 'yan jarida cewa, a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, asusunsa da kasar Sin sun yi hadin gwiwa kan magance da yaki da cutar AIDS, tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro. Ana fatan a nan gaba, asusun zai ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin yaki da cututtuka masu yaduwa, da cin gajiyar musayar fasahohi don amfanawa al'ummomin kasashen duniya. (Zainab)