in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da mataimakin babban sakataren MDD
2015-05-05 09:52:29 cri

A jiya Litinin da yamma ne a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da mataimakin babban sakataren MDD kuma darektan gudanarwa na shirin yaki da cutar AIDS na MDD Michel Sidibe, da kuma darektan gudanarwa na asusun yaki da cutar AIDS da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro Mark Dybul.

Firaminista Li Keqiang ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai kan aikin yaki da cutar AIDS, kana tana kara karfin matakan da ta ke dauka da zuba jari kan wannan aiki, domin koyon fasahar jinya da kara kula da wadanda suka kamu da cutar AIDS, ta yadda za a kawar da bambancin da ake nuna wa wadanda suka kamu da cutar.

Mr. Li ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa, yana fatan hukumomin da abin ya shafa na MDD za su nuna taimakawa kasar Sin a fannonin kudade da fasaha da sadarwa da aikin nazari, domin kara wa kasar Sin karfin rigakafin cutar AIDS da kuma kawar da ita kwata-kwata. Kana yana fatan za a kara nuna goyon baya ga hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afrika wajen harhada magunguna domin kawo moriya ga jama'arsu.

A nasu jawabin Michel Sidibe da Mark Dybul sun bayyana cewa, ba ma kawai gwamnatin Sin ta yi kokarin ingiza bunkasuwar tattalin arziki ba, har ma ta dora muhimmanci sosai kan lafiyar jama'a, hakan ya zama abin koyi ga sauran kasashe masu tasowa da dukkan fadin duniya. Shirin yaki da cutar AIDS na MDD da asusun yaki da cutar AIDS sun nuna jinjina ga matakai masu yakini da gwamnatin Sin ta dauka wajen kawar da cutar AIDS, suna masu cewa, wadannan matakai sun samar da sakamako mai kyau.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China