in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga kasa da kasa da su samar da gudummawa ga kasashen tsakiya da yammacin Afirka wajen yaki da ta'addanci
2016-07-28 16:01:07 cri
Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya da su nuna goyon baya ga kasashen tsakiya da yammacin nahiyar Afirka, ciki har da kasashen dake yankin tafkin Chadi wajen yaki da ta'addanci.

Wu Haitao ya bayyana cewa, yaki da ta'addanci da ake gudanarwa a Afirka, wani muhimmin kashi ne cikin ayyukan yaki da ta'addanci a kasa da kasa. Don haka kamata ya yi kasashen duniya su nuna goyon su ga wannan aiki, don tabbatar da sojojin kasa da kasa sun gudanar da ayyuka, da kawar da barazanar ta'addanci da ake fama da ita a kasashen dake yankin tafkin Chadi.

Ya ce kamata yayi kasashen duniya su kara yin hadin gwiwa tare da kungiyar AU, da ECOWAS, da kwamitin kula da harkokin yankin tafkin Chadi wajen warware matsaloli a yankin, ta hanyar yin shawarwari da shiga-tsakani. Kaza lika a cewar sa kasar Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da kasashen duniya musamman wadanda abun ya shafa, wajen nuna goyon baya ga kasashen tsakiya da yammacin Afirka, a yunkurin su na cimma burin samun zaman lafiya da wadata mai dorewa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China