Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya shedawa manema labarau cewar WFP ya tabbatar da cewar, matsalar karuwar dumamar yanayi na El Nino shine ummul aba isin daya haddasa matsalar ta fari a yankunan, kuma tuni matsalar ta fara shafar kayan amfanin gona.
Acewar WFP, makatsalar zatafi kamari ne a kasashen Malawi, da Madagascar da kuma Zimbabwe. Tuni kasar Lesotho ta kaddamar da wani shirin daukin gaggawa game da matslar fari a watan daya gabata, kuma kusan kashi daya bisa uku na alummar kasar basu da wadataccen abinci.
Haq, yace sauran kasashe da matsalar ta shafa sune Angola, Mozambique, da da kuma Swaziland.
Ita dau matsalar ta El Nino, tana haifar da kamfar ruwan sama a fadin yankin na kudancin Afrika tun a shekarar bara, lamarin da ya haifar da bushewar amfanin gona. A baya dai Afrikan ta kudu na fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen ketare, amma a halin yanku tana bukatar shigo da kayan abinci kimanin tone miliyan 5 zuwa 6 na masara daga kasashen ketare a sakamakon wannan matsala.