Wani rahoton hasashen ci gaban tattalin arziki da asusun IMF ya fitar, ya nuna cewa a kwanakin baya saurin bunkasuwar tattalin arziki na kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara na shekarar 2015 ya kai kashi 3.5 cikin dari, kuma an yi hasashen cewa wannan adadi zai yi kasa zuwa kashi 3 cikin dari a shekarar nan ta 2016, adadin da ya yi kasa cikin sauri ga kusan kasashe 10, wanda a baya adadin ya kai kashi 6 cikin dari.
Rahoton ya nuna cewa a shekarar nan ta 2016, tattalin arzikin wannan yanki ya ci gaba da tabarbarewa, kana kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara na fuskantar kalubale sosai kan yadda za su farfado da shi.
Asusun IMF ya bayyana cewa, cikin kankanen lokaci a nan gaba, kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara na iya gamuwa da wahalhalu a fannin bunkasa tattalin arzikin su, amma ba a rasa karfin bunkasa tattalin arzikin kamar yadda aka fuskanta cikin shekaru 10 da suka gabata, musamman ma karuwar yawan mutane da kuma kyautata muhallin kasuwanci, matakan da za su ingiza bunkasuwar tattalin arziki a matsakaicin lokaci nan gaba.(Lami)