Taken taron dai shi ne, makomar shigar da kudin Yuan na Sin a tsarin IMF a matsayin halaltaccen kudi a tsarin kudaden ba da lamani.
Kasar Sin ta kasance a matsayin babbar abokiyar huldar kasuwanci da zuba jari a fannin samar da ababan more rayuwa da iskar gas da albarkatun man fetur da kasashen Afrika.
A wata sanarwar da babban bankin kasar Tanzaniya ya fitar a jiya Asabar ta nuna cewa, taron zai kuma tabo batun tasiri da kuma rawar da manyan bankunan kasashen za su taka game da ci gaban kananan bankuna raya sana'o'i da hada hadar kudade a yankunan.
Sanarwa ta kara da cewar mahalarta taron za su hada da gwamnonin manyan bankuna da na kanana da kuma sauran hukumomin al'amuran kudi na kasashen gabashi da kudancin Afrika. (Ahmad Fagam)