Madam Lagarde ta bayyana haka ne a wani bikin nuna sabbin fasahohi da ya gudana a jihar Colorado ta kasar Amurka a jiya Lahadi, inda ta ce matakan da jami'an kasar Birtaniya da na kungiyar EU za su dauka a kwanaki masu zuwa za su tabbatar da yanayin da za a fuskanta a duk duniya. Don haka, a cewarta, asusun IMF ya sake bukatar bangarorin da abun ya shafa da su dauki matakan da suka dace wadanda za a iya hasashensu, don sassauta yanayin rashin tabbas, da tabbatar da gudanar aikin cikin zaman lafiya.
A cewar shugabar asusun IMF, da ma kasuwannin hada-hadar kudi ba su zaci cewa za a shiga wani babban yanayi mai hadarin gaske ba sakamakon ballewar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai, amma bayan da aka sanar da sakamakon zaben raba gardama a kasar Birtaniya matakin ya tayar da zaune-tashi a kasuwannin hada-hadar kudi na kasashe daban daban, har ma darajar musayar kudin Fam na kasar Birtaniya ta ragu da kimanin kashin 10%. Duk da haka, bai girgiza kasuwannin hada-hadar kudi ba, kana manyan bankunan kasashe daban daban sun shirya don kara samar da kudaden da ake bukata a kasuwanni.(Bello Wang)