Kasar Namibiya na shirin soke wani wajabcin rike da takardar visa ga dukkan 'yan Afrika bisa tunanin dunkulewar Afrika, in ji shugaban kasar Hage Geingob, a ranar Litinin, bayan da ya jagoranci bikin bude zaman taron siyasar waje ta kasar, tare da bayyana cewa, "'Yan uwanmu maza da mata na nahiyar Afrika za su kasance wadanda ake murnar zuwansu a kasar Namibiya har kullum. Mun dauki niyyar fadada wannan alfarma ga dukkan masu rike da takardar visa ta kasashen Afrika ta hanyar ba su da farko visa da zuwansu da kuma soke wajabcin rike da takarar visa." (Maman Ada)