Gundumar kasar Sin ta rabbata hannu kan yarjejeniyar abokantaka tsakanin ta da wani yanki na Namibiya
Jami'ai daga gundumar Jiangsu da yankin tsakiya na Khomas a kasar Namibiya sun rattaba hannu kan yarjejeniya a hukumance ranar Jumma'ar nan na kafa huldar abokantaka tsakanin bangarorin biyu.
Yarjejeniyar dai gwamnar yankin Khomas ce Laura Mclaud-Katjirua da Gwamnan gundumar Jiangsu Li Xueyong suka rattaba hannu akai.
Yarjejeniyar na da zummar karfafa fahimtar juna da habaka mu'amalar abota na hadin gwiwwa tsakanin bangarorin biyu.