in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin kasar Sin sun samar da ayyukan yi 6,000 a Namibiya
2015-08-19 11:29:35 cri

Jakadan kasar Sin a Namibiya ya ce kamfanonin kasarsa a yanzu haka sun samar da ayyukan yi ma mazauna 6,000.

Da yake hira da kamfanmin dillanci labarai na Sin na Xinhua, Jakada Xin Shunkang ya ce, ciniki a tsakanin kasashen biyu yana da armashi kwarai yayin da kasar Sin ta zuba jarinta ya taimaka wajen habaka cigaban masana'antu a kasar Namibiya, ita kuma a nata bangaren Namibiya ta taimaki Sin ta hanyar bunkasa kasuwanninta.

A cewar Jakadan, akwai kusan kamfanonin kasar Sin 46 dake aiki a Namibiya ta hanyar tattalin arziki karkashin jagorancin Swakop Uranium wanda ya zuba jarin dalar Amurka biliyan 2.5 a mahakar Husab wanda ya yi fice a duniya.

Baya ga hakar ma'adinai, kamfanonin Sin sun kuma zuba jari a sauran sana'o'i kamar kere-kere, aikin gona da kuma gine-gine.

Jakada Xin ya ce, kasar Namibiya ta zama daya daga cikin abokan cinikin kasar Sin mafi muhimmanci a cikin kasashen Afrika.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China