A yayin bikin, shugaban kasar Hage Geingob ya yaba wa matakin ba da kudin kyauta da Sinawa 'yan kasuwa suka dauka, kuma ya nuna godiya da yabo ga asusun jin kai na Sinawan dake zaune a kasar Namibiya. Sannan ya sa kaimi ga dalibai wadanda suka samu kudin tallafi da su yi kokarin koyon ilmi, ta yadda za su iya zama wakilai masu sada zumunta tsakanin kasashen Namibiya da Sin, kuma yana fatan su dawo Namibiya bayan da suka kammala karatunsu a kasar Sin.
Mr. Huang Yuequan, shugaban asusun jin kai na Sinawa ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu yawan daliban da suka samu kudin tallafi ya riga ya kai 34, kuma yawan kudin tallafi da asusun ya kebe ya kai kudin Sin yuan miliyan 5, wato kimanin dalar Amurka dubu dari 8. (Sanusi Chen)