in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a fara shigowa da naman shanu daga kasar Namibiya zuwa kasuwannin Sin
2015-08-14 10:20:04 cri
Rahotanni daga Windhoek na kasar Namibiya ya ce nan ba da dadewa ba za'a fara shigowa da naman shanun kasar zuwa kasuwannin kasar Sin sakamakon yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba ma hannu a farkon wannan watan game da tsarin tafiyar da harkokin cinikin.

Ministan ayyukan gona na kasar Namibiya John Mutorwa ya sanar da cewar kasuwannin shanu na kasar da kamfanoni bada dadewa ba zasu shiga fagen mafi girma na kasuwanni a wannan fanni a duniya baki daya, abin da ya sa kasar ta Namibiya ta zama kasar Afrika ta farko da zata fitar da nama da kashi na shanu zuwa kasar Sin.

Wannan yarjejeniya dai na fitar da naman shanu tun a shekara ta 2011 ne aka fara tattauna shi kuma kasar ta yi matukar sa'a na zama cikin kasashe 10 a duniya da yanzu aka amince su fitar da naman shanu su zuwa babban kasuwa ta duniya wanda hakan ya nuna amincewar da aka yi da tsarin kiwon lafiyar dabbobi da ake da shi a kasar inji Minista John Mutorwa.

Kasuwannin kasar Sin dai ba kamar kasuwannin nahiyar Turai ba sun amince da shigowa da naman shanu da kashi.

A yanzu haka kasar tana fitar da metric tan 17,000 na naman shanu zuwa kasar Afrika ta kudu a duk shekara, metric tan 10,000 kuma zuwa yankin Turai. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China