A gun taron manema labaru da aka gudanar, Joseph Biden ya bayyana cewa, ba ma kawai sun yi shawarwari kan yadda za a yi nasara a yaki da kungiyar IS ba, har ma sun yi shawarwari kan kara nuna goyon baya ga jam'iyyar da ke adawa da gwamnatin Syria da mika ikon mulkin kasar. Ya ce, ban da haka, bangarorin biyu sun tabo maganar horar da kuma bayar da makamai ga kungiyoyin da ke adawa da gwamnatin Syria masu sassaucin ra'ayi.
Dadin dadawa, Joseph Biden ya kara da cewa, Amurka tana bukatar samun goyon baya daga Turkiya domin yaki da kungiyar IS.
A nasa bangare, Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, Turkiya za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da Amurka a fannin yaki da kungiyar IS, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a wannan yanki.(Fatima)