in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayar da sanarwa game da hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin
2016-07-14 15:04:44 cri
Kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayar da sanarwa game da hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin, inda ya bayyana cewa,

Na farko, Wannan sanarwa da sanarwar da gwamnatin kasar Sin ta bayar game da ikon mallaka da moriyar teku kan tekun kudancin kasar Sin sun bayyana matsayin kasar Sin, hukuncin da aka yanke game da wannan batu ba shi da wata ma'ana ko kadan. Kuma kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya tsaya tsayin daka kan wannan manufa.

Na biyu, Sin tana da ikon mallakar tsibiran dake tekun kudancin kasar Sin, da wadanda suke a yankin teku, yankunan dake dab da su, da kuma yankunan hada hadar tattalin arziki na musamman. Sin tana da iko kan tekun kudancin kasar Sin. Duk wata kasa ko hukuma ba ta da iznin raina ikon mallaka da moriyar teku na kasar Sin kan tekun kudancin kasar.

Na uku, kasar Philippines ta bayar da batun yanke hukunci da kanta, wanda ya keta yarjejeniyar daidaita batutuwa ta hanyar yin shawarwari tsakanin Sin da Philippines, da sanarwar ayyukan bangarorin dake tekun kudancin Sin, da yarjejeniyar dokokin teku ta MDD, kuma ba ta yi amfani da kudurin yanke hukunci cikin adalci ba, ta keta ikon kasar Sin na zaben hanyar daidaita rikici a matsayin wata kasa mambar da ta daddale yarjejeniya, tare da hallaka cikakken ikon yarjejeniya.

Hukumar yanke hukunci kan batun tekun kudancin Sin da aka kafa bisa bukatar Philippines ba ta da ikon yanke hukunci kan wannan batu, ta yi biris da tarihi da hakikanan abubuwa dangane da tekun kudancin Sin, tare da amfani da ikon yarjejeniyar ba bisa adalci ba, ta yanke hukunci kan batun ta haramtacciyar hanya, har ma ta keta dokokin duniya da ka'idojin yanke hukunci na duniya, shi ya sa sakamakon da ta fitar ba shi da wani amfani. Sin ba ta amince da wannan sakamako ba. (Zainab,Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China