Zancen wai samun goyon baya daga kasa da kasa kan hukuncin da kotu ta yanke game da tekun kudancin Sin hanyar Amurka ce ta ruruta rikicin
Bayan da aka bayyana sakamakon hukuncin da kotu ta yanke game da tekun kudancin kasar Sin, lamarin ya jawo hankali sosai a kasar Philippines, inda wasu suka bayyana cewa, abin da aka fada cewa wai an samu goyon baya daga kasa da kasa ga hukuncin ba gaskiya ba ne. Tsohon jami'in diplomasiyya na kasar Philippines kuma tsohon babban sakataren cibiyar harkokin teku ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Alberto Encomienda ya bayyana wa 'yan jarida cewa, zancen wai samun goyon baya daga kasa da kasa ga hukuncin hanyar ce da kasar Amurka take bi don neman ruruta rikicin.
Encomienda ya bayyana cewa, ya nuna shakku ga abin da aka fada cewa an samun goyon baya daga kasa da kasa kan hukuncin, a ganinsa ita ce hanyar ruruta rikici ta kasar Amurka. Idan aka dubi sanarwar diplomasiyya da kasar Amurka ta gabatar a baya game da kutsa kai cikin kasar Libya da Iraki, za a ga ita ma ta bayyana cewa matakin na samun goyon baya daga kasa da kasa. Don haka, a cewar tsohon jami'in kasar Philippines zancen wai an samu goyon baya ga hukuncin da aka yanke game da tekun kudancin Sin yana daya daga cikin zantuttukan da Amurka ta fada, don haka ya nuna shakku ga sahihancin irin wannan goyon baya wanda Amurka ta ce aka samu. (Zainab)