in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: gwamnatin kasar Sin ta bayar da sanarwa kan 'yancin da take da shi a yankin tekun kudancin kasar da kuma yankin baki daya
2016-07-12 21:03:30 cri

A yau Talata 12 ga wata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi jawabi kan sakamakon hukuncin da aka yanke game da batun tekun kudancin kasar Sin, inda ya bayyana cewa, a yau, an kafa wata kotun wucin gadi don yanke hukunci kan batun tekun kudancin kasar Sin bisa rokon da tsohuwar gwamnatin kasar Philippine ta yi bisa kashin kanta, da nufin keta 'yancin da kasar Sin ke da shi a yankin. Game da wannan, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta riga ta ba da sanarwa kan cewa, kasar Sin ba ta amince kuma ba ta yarda da hukuncin da aka yanke kan batun ba. Ga rahoton da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

Wang Yi ya nanata cewa, tun da farko batun yanke hukunci kan tekun kudancin kasar Sin wasa da hankali ne a siyansace, wadda aka yi bisa hujjan cewa, wai an yi shi ne bisa doka. Wang Yi ya ce, "Wannan wani shiri ne na nuna karfi a cikin wannan yankin, wanda aka aikawa ba tare da samun amincewa daga wajen sassan da abin ya shafa ba, tsohowar gwamnatin kasar Phillippines ta saba wa sharadin daidaita takkadama ta hanyar yin shawarwari, kuma ta karya alkawarin da ta dauka a cikin 'sanarwar da sassan batun tekun kudancin Sin ya shafa', inda ta gabatar da kara ita kadai a gaban wata kotun yanke hukunci. A fili yake cewa, ta dauki wannan mataki ne ba domin tana son kawar da takkadamar a tsakaninta da kasar Sin kamar yadda ya kamata ba, tana son keta 'yancin kasar Sin da kuma mamaye yankuna da muradun kasar Sin a yankin tekun kudancin Sin, har ma tana son lalata halin zaman lafiya da kwanciyar da ake ciki a yankin."

Game da wannan karar da bangaren Phillippines ya gabatar bisa radin kansa kawai, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayinta na kin yarda, da halarta ko amincewa, balle ma ta martaba wannan hukunci. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin ta dauki wannan matsayi ne domin tana kokarin mutunta dokokin kasa da kasa da ka'idojin da ake bi a yankin. Wang Yi ya nuna cewa, "Bisa dokokin kasa da kasa, kowace kasa tana da 'yancin zabar hanyar daidaita takkadama, kuma bisa yarjejeniyar dake shafar harkokin teku ta MDD, ba za a iya tilastawa kowace kasa mambarta da ta martaba ajandar da ba ta amince ba. Bisa 'yarjejeniyar sassan da ke shafar tekun kudancin Sin' da kasar Sin da kasashe 10 na kungiyar Asean suka kulla, ya kamata kasashen da batun ya shafa su daidaita takkadamar dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari kai tsaye. Sakamakon haka, kasar Sin ta dauki matsayin kin amincewa, kuma ta ki shiga ajandar yanke hukunci, wannan yana dacewa da yarjejeniyar dake shafar harkokin teku ta MDD. Kasar Sin na aiwatar da harkoki bisa doka."

Game da abin da ka iya biyo baya a yankin tekun kudancin Sin bayan hukuncin da aka yanke bisa bukatar kasar Philippines, Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba dokokin kasa da kasa wajen daidaita takkadamar dake tsakaninta da sassan da abin ya shafa ta hanyar yin shawarwari kai tsaye cikin lumana. Sannan za ta ci gaba da tabbatar da yin zirga-zirgar jiragen ruwa da na sama na kasashen duniya a yankin cikin 'yanci. Bugu da kari, za ta ci gaba da tsayawa kan matsayin aiwatar da "sanarwar sassan da batun tekun kudancin Sin ya shafa" kamar yadda ake fata, ta yadda za ta yi kokarin ingiza yin shawarwari kan "ka'idojin daukar matakai da za a bi a yankin tekun kudancin Sin". Wang Yi ya nuna cewa, "Yanzu maganar wasa da hankali ya wuce, yanzu lokaci ne da ya kamata a koma ga maganar zahiri. Kasar Sin ta lura da jerin bayanai da sabuwar gwamnatin kasar Philippines ta gabatar a 'yan kwanakin nan, ciki har da aniyarta ta maido da shawarwari tare da kasar Sin kan batun tekun kudancin kasar Sin. Kasar Sin na sa ran ganin yadda sabuwar gwamnatin Phillipines za ta dauki matakan da suka dace wajen kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da warware sabanin da ke tsakaninsu yadda ya kamata, a kokarin ciyar da huldarsu gaba." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China