Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin shi ne ya bayyana hakan yau, a yayin da yake gabatar da wannan takarda a taron manema labarai da ya gudana a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Ya ce, matakin da kasar Phillippines ta dauka babu abin da zai haifar illa kara tsananta takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu kan batun tekun kudancin kasar ta Sin.
Ita dai wannan takarda mai take, "Kasar Sin tana kan matsayinta na daidaita wannan batu ta hanyar sasanta takaddamar dake tsakaninta da kasar Philippines kan batun tekun kudancin kasar Sin" an wallafa ta ne kwana guda bayan da wata kotu ta yanke hukunci kan wannan batu bisa bukatar tsohuwar gwamnatin kasar Philippines.
Liu ya bukaci sauran kasashe da kada su yi amfani da wannan dama wajen yiwa kasar Sin barazana. Kasar Sin tana fatan sauran kasashe za su yi kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwancikyar hankali a yankin tekun kudancin kasar Sin, maimakon barin yankin ya fada cikin yaki.
Bugu da kari, mataimakin ministan ya bayyana cewa, kasar Sin ta dage 'yancin yin zirga-zirga ta sama a yankin tsaron da ta shata a yankin, saboda barazanar da yankin yake fuskanta a halin yanzu. (Ibrahim)