Shugaba Xi ya fadi haka ne yayin da yake ganawa da shugaban majalisar kungiyar tarayyar kasashen Turai Donald Tusk da shugaban majalisar zartarwas kungiyar EU Jean-Claude Juncker, wadanda suka zo kasar Sin don halartar taron ganawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 18. Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta amince da ko wane ra'ayi da matakin da za a dauka bisa sakamakon wannan hukuncin ba. Ko da yaushe kasar Sin ta kan kiyaye dokokin kasa da kasa da kuma adalci, sannan tana tsayawa tsayin daka kan bin hanyar samun ci gaba cikin lumana. Kasar Sin za ta dukufa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin kasar, da kuma warware sabanin da ke tsakaninta da sauran kasashe ta hanyar shawarwari cikin lumana, bisa tushen girmama tarihi da kuma dokokin kasa da kasa. (Kande Gao)