Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Lu Kang ya amsa tambayoyin manema labaru game da ra'ayin da ministan harkokin waje na kasar Japan ya dauka kan sakamakon hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin Sin cewa, yana fatan kasar Japan za ta yi la'akari da huldar dake tsakaninta da kasar Sin da kuma kwanciyar hankali a yankin, kana ya kamata ta daina tsoma baki kan batun tekun kudancin Sin, kada ta ci gaba da yin abin kuskure.
Mr. Lu Kang ya kara da cewa, kasar Japan ta san tarihin tekun kudancin Sin. Ya kamata ta girmama tsarin duniya da aka kafa tun bayan babban yakin duniya na biyu. Yana fatan kasar Japan za ta kara la'akari da huldar dake tsakaninta da kasar Sin da kuma kwanciyar hankali a yankin, ya kamata ta daina tsoma baki kan wannan batu.(Lami)