Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ne ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai, bayan da wasu kasashe suka bayyana cewa, wajibi ne kasar Sin ta martaba hukuncin da kotun ta yanke kan batun tekun kudancin Sin wadda kasar Phillippines ta shigar bisa radin kanta.
Lu ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta amince da matakin da wadannan kasashe uku ko hudu suka dauka ba. Ta ce, kasashen duniya da dama sun nuna goyon bayansu ga kasar Sin kan matakin da ta dauka ta fuskoki daban-daban.
Kasar Sin ta sha nanata matsayinta kamar yadda dokokin teku na MDD suka tanada dangane da daidaita takaddamar da ta shafi shata kan iyakar teku, maimakon matakan tilastawa kasa wajen sasanta takaddama.
Kakakin ya ce, baya ga kasar Sin akwai kasashe da dama da suka shigar makamancin wannan koke. Daga cikin kasashen nan biyar da ke da kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, hudu daga cikinsu sun yi haka, yayin da daya kasar ba ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya ba.
Haka kuma, daga cikin kasashen kungiyar G7 wadanda suka soki lamarin kasar Sin game da batun tekun kudancin Sin, hudu daga cikinsu sun gabatar da irin wannan koke, kana daya daga cikinsu ita ma ba ta sanya hannu a kan wannan yarjeeniyar teku ta MDD ba.
A saboda haka, kamata ya yi kasashen uku ko hudu su martaba dokokin kasa da kasa yadda ya kamata, maimakon su rika wasa da ita.
Lu Kang ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da martaba dokokin MDD, kare 'yancin yankunanta na kasa da na teku, tare da ci gaba da neman warware takadda ta hanyar lumana. (Ibrahim)