in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta shawarci kasashen da abin ya shafa da su daidaita batun tekun kudancin Sin ta hanyar yin shawarwari cikin lumana
2016-07-12 13:52:06 cri
A jiya Litinin ne, ma'aikatar hadin gwiwa da harkokin waje ta Benin ta ba da sanarwa kan batun tekun kudancin Sin, inda ta ba da shawara ga kasashen da abin ya shafa da su daidaita batun ta hanyar yin shawarwari, musamman ma ta hanyar diplomasiyya a tsakaninsu.

Sanarwar ta ce, gwamnatin Benin ta nanata matsayinta na tabbatar da zaman lafiya a duniya. A sabili da haka, gwamnatin kasar ta nuna goyon baya ga gwamnatocin Sin da ta Philippines da su tattauna da yi kokarin daidaita wannan batu ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, musamman ma ta hanyar diplomasiyya. Gwamnatin Benin za ta ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya tare da sauran kasashe baki daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China