Bugu da kari, ya ce, yanzu haka an samun karin kasashen duniya da suka nuna goyon baya kan matsayin kasar Sin kan wannan batu, inda suke sa ran bangarorin biyu da batun ya shafa za su warware batun tekun kudancin kasar Sin ta hanyar yin shawarwari, kana, suna fatan za a bar kasashe masu 'yanci su zabi tsarin warware sabani da kansu, kuma wadanda suka goyi bayan kasar Sin ba su samu goyon bayan gamayyar kasa da kasa ba, sabo da kasar Sin ce kasa mai kare dokokin kasa da kasa.
Tun lokacin da aka shiga watan Yuli, kasashe da dama da suka hada da Cambodia, Angola, Liberia, Madagascar da kuma Senegal da dai sauransu sun ci gaba da nuna fahimtarsu da nuna goyon baya ga kasar Sin kan wannan batu. (Maryam)