Ma'aikatar harkokin wajen Kenya ta ambata cewar abu mafi muhimmanci da zai kawo karshen takaddama kan batun na tekun kudancin Sin shi ne, kasashen da abin ya shafa su warware rikicin ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin wanda ke kunshe cikin daftarin yarjejeniyar da kasar Sin da kungiyar kasashen kudancin Asiya suka rattaba hannu kanta tun a shekarar 2002.
Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Zimbabwe ta bayyana irin wannan ra'ayi tana mai cewa, wannan ita ce kadai hanyar da za'a samu maslaha wajen kawo karshen tangarda tsakanin kasashen yankin da abun ya shafa.
A yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, minsitan harkokin wajen kasar Saliyo, Samura Kamara ya jaddada muhimmancin kasashen da abun ya shafa su mutunta junansu, kuma su kiyaye 'yancin kasa da kasa kamar yadda ke kunshe cikin dokokin MDD da suka shafi takaddama kan tekun kasashen duniya.
Ministan ya bukaci hukumomin shari'a na kasa da kasa da su martaba 'yancin da kasashen duniya ke da shi karkashin doka ta 298 a cikin dokokin MDD game da teku.
Ya jadda cewar kasar Saliyo tana goyon bayan kasar Sin 100 bisa 100 wajen daukar matakan tattaunawar sulhu wajen warware takaddamar game da tekun kudancin kasar.
Sashen kula da hulda da kasa da kasa na Afrika ta kudu ya bayyana cewar, kasar Afrika ta kudun tana goyon bayan ra'ayin baiwa kasashe masu 'yancin kansu warware duk wani sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa, wanda hakan zai iya tabbatar da samun zaman lafiya mai dorewa game da takaddama kan tekun kudancin kasr Sin. (Ahmad Fagam)