Wannan sanarwa ta nuna cewa, tun fil azal, tsiriban Nansha yankunan kasar Sin ne. A cikin dogon lokaci bayan yakin duniya na 2, babu kasancewar takkadama kan yankin tekun kudancin Sin. Amma a shekaru 70 na karnin da ya gabata, an gano arzikin man fetur da iskar gas a yankunan tekun kudancin Sin, sakamakon haka, wasu kasashe ciki har da kasar Phillippines suka mamaye wasu kananan tsibiran kasar Sin dake yankin teku na Nansha ba tare da samun izini ba, wannan shi ne asalin dalilin da ya sa aka samu takkadama kan yankin tekun kudancin Sin.
Wannan sanarwa ta kuma zargi gwamnatin kasar Phillippines da kin yin amfani da darusan "yarjejeniya kan dokokin dake shafar teku ta MDD", har ma ta gabatar da maganar neman yanke hukunci kan yankin tekun kuddancin Sin ita kadai a kokarin samun ikon mulkin tsibiran da ta mamaye a da ba bisa doka ba, da kuma musunta ikon halal da moriyar halal na kasar Sin a yankin tekun kudancin Sin.
Daga karshe, sanarwar ta bayyana cewa, wasu kasashe suna neman mayar da kasar Sin saniyar ware bisa wannan maganar neman yanke hukunci kan batun yankin tekun kudancin Sin, amma ba za su cimma burinsu ba. Yanzu yawan kasashen da suke goyon bayan matsayin da kasar Sin take dauka yana ta karuwa. Ya kamata kasashen da suke yankin tekun kudancin Sin su daidaita matsalolin dake kasancewa a tsakaninsu da kasar Sin ta hanyar yin shawarwari kai tsaye cikin lumana a tsakaninsu da kasar Sin. Kasar Sin da kasashen Asiya, suna iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin Sin ta hanyar yin hadin gwiwa tsakaninsu. (Sanusi Chen)