Mr. Encomienda ya kara da cewa, dalilin da ya sa suka ingiza a yanke wannan hukunci shi ne suna tsammani za su samu moriya daga wannan hukunci, amma ainihin burin da suke son cimmawa shi ne biyan bukatunsu na siyasa. A ganin Alberto Encomienda, babu wata hujja da ta sa kasar Japan za ta tsoma baki kan batun tekun kudancin Sin. Amma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Amurka ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an yanke hukunci kan maganar dake shafar yankin tekun kudancin Sin. (Sanusi Chen)