Shugaban kwamitin gudanarwa na asusun musayar ilmin doka na Sin da Australia, kana babban lauya mai izni na babbar kotun Hongkong, Ma Enguo ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a jiya Litinin cewa, batun tekun kudancin kasar Sin, wani irin rikici ne dake shafar ikon mallakar tsibiran yankin tekun da sauransu tsakanin Sin da Philippines. Bisa yarjejeniyar dokar teku ta MDD, da zarar rikicin yankin teku ya shafi ikon mallakar kasa, sai hukumar yanke hukunci kan batun yankin teku ba ta da ikon kulawa a kai.
Mataimakin shugaban asusun, lauya Qian Zhiyong ya nuna cewa, Philippines ta fidda wannan hukunci da kanta, Sin ba za ta karba ba, ba za ta shiga batun ba. Idan Sin ba za ta shiga wannan batu ba, duk ayyukan da za a yi ba za su dace da dokoki ba.(Fatima)