Rahotanni na nuna cewa, kasar Philippine ta bayyana a cikin hukuncin da aka yanka game da tekun kudancin kasar Sin cewa, Sin ba ta da ikon mallakar tsibirin Meiji da sauran tsibiran da ke yankin tekun kudancin Sin. Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Juma'a cewa, Sin tana da ikon mallakar tekun kudancin kasar Sin da sauran tsibiran dake yankin.
Hong Lei ya bayyana cewa, akwai matsala a tsakanin tsibiran dake tekun kudancin kasar Sin da tekun kasar Philippines a fannin moriyar teku. Sin tana son samun sakamako mai adalci kan iyakan teku a tsakaninta da Philippines ta hanyar yin shawarwari bisa tushen tarihi da yarjejeniyar dokar teku ta MDD da sauran dokokin kasa da kasa. (Zainab)