Miliyoyin 'yan Birtaniya ne suka jefa kuri'unsu a rumfunan zabe kimanin 41,000 a jiya Alhamis a matsayin zaben raba gardama na yiwuwar ballewar Birtaniya ko cigaba da zama mamba a kungiyar tarayyar Turai wato EU.
An dai fara zaben ne tun da sanyin safiya da misalin karfe 7 wato karfe (0600 agogon GMT), sai dai runfunan zaben da dama basu bude da wuri ba, sakamakon ruwan sama da aka yi cikin dare a birnin Landan da ma yankunan kudu maso gabashin Ingila.
Za'a bayyana sakamakon zaben cikin dare, sai dai sakamako na karshe na zaben za'a bayyana shi ne a hukumance a babban dakin taro na Manchester Town Hall, kuma mai yiwuwa a bayyana shi da safiyar yau Juma'a agogon kasar.
Wata kididdiga da hukumar zaben kasar ta fitar ta nuna cewar mutane miliyan 46 da rabi ne suka cancanci kada kuri'u a zaben kuri'ar raba gardaman.