Kafin haka, mista Schulz ya jagoranci taron shugabannin jam'iyyun dake da kujerunsu a majalisar Turai, inda aka tattauna batun jefa kuri'ar raba gardama da aka yi a kasar Birtaniya don ganin ko za a balle kasar daga EU ko akasin haka. Daga bisani, Schulz ya gaya ma manema labaru cewa, za a zartas da kuduri a taron musamman da za a kira a birnin Brussels, daga baya za a mika kudurin ga taron shugabannin kungiyar EU dake tafe.
A cewar mista Schulz, yana bakin ciki matuka kan yadda jama'ar Birtaniya suka tsai da kudurin ballewar kasarsu daga EU, amma wannan niyya ce ta daukacin jama'ar kasar. Wannan lokaci ne mai wuya matuka ga kungiyar EU gami da kasar Birtaniya. Sai dai yanzu za a share fagen matakan za a za a dauka a nan gaba daga fannonin shari'a da na tsarin aikin.(Bello Wang)