A yau Jumma'a 24 ga wata da safe, agogon kasar Birtaniya, kwarya-kwaryar sakamakon da gwamnatin kasar Birtaniya ta fitar ya nuna cewa, zaben raba gardamar da aka gudanar a ranar 23 ga wata a kasar ta Birtaniya dangane da ko kasar za ta ci gaba da kasancewa a kungiyar tarayyar Turai ko akasin haka, yanzu haka 'yan kasar sun zabi ficewa daga kungiyar. Kididdigar da aka yi ta nuna cewa, wadanda suka nuna goyon bayan ficewa daga kungiyar ya kai kashi 52%, a yayin da wadanda suka nuna rashin amincewa ya kai kashi 48%.
A wannan rana, jagoran jam'iyyar UK Independence Party Nigel Paul Farage, wanda har kullum yake nuna cikakken goyon baya ga ficewar kasar daga tarayyar Turai ya bayyana cewa, Birtaniya za ta rungumi ranar samun 'yancin kanta.
A wannan rana, sakamakon rashin samun tabbas ne, darajar kudin fam na kasar ya yi faduwar da bai taba yi ba tun a shekarar 1985.(Lubabatu)