A wata sanarwar da kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanar Sani Usman ya bayar a ranar Lahadi, ya ce, wadannan 'yan Boko Haram sun kai wannan harin ne a ranar Juma'ar da ta gabata, tare da daukar wasu manyan makaman da suka hada da nakiyoyi.
A cewarsa, bangarorin 2 sun kwashe wasu sa'o'i suna musayar wuta, kafin a karshe sojojin kasar suka samu damar dakile dakaru 'yan Boko Haram.
Usman ya kara da cewa, akwai 'yan Boko Haram da dama da suka tsira, amma sun samu raunuka. Yayin da a bangaren sojojin kasar, an samu wasu 2 da suka rasa rayukansu, gami da wasu 5 da suka samu raunukan irin daban daban.
Haka zalika, kakakin ya ce, sojojin kasar sun kwace wata babbar bindiga mai sarrafa kanta, da gurneti mai hade da roka, da harsasai, yayin da aka kama wasu 2 daga cikin 'yan ta'addan da suka kaddamar da wannan hari da ransu.(Bello Wang)