Ministan harkokin wajen Saliyo ya tafi Najeriya a kokarin ceto jami'in diplomasiyar kasar da aka sace
Wata tawaga mai karfi karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Saliyo Samura Kamara tana shirin ganawa da mahukuntan Najeriya, domin lalubo hanyoyin ceto jami'in diplomasiyar kasar ta Saliyo Claude Nelson-Williams da wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da shi.
Ministan watsa labarai na kasar Saliyo Mohamed Bangura ya shaidawa manema labarai cewa, a jiya ne tawagar ta bar kasar zuwa kasar ta Najeriya.
A makon da ya gabata ne dai aka sace Nelson –Williams a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja domin halartar bikin faretin yaye sojoji.(Ibrahim)