Mai alfarma sarkin musulmi, kuma shugaban majalisar koli ta addinin musulunci Sultan na Sokoto, Alhaji Sa'ad Abubakar III, shi ne ya sanar da hakan, ya ce ba'a samu ganin jinjirin watan Shawwal ba a dukkan fadin Najeriya.
Sakamakon hakan, ya umarci al'ummar musulmin kasar dasu gudanar da azumi a yau Talata, kuma su gudanar da Idin karamar sallah a gobe Laraba.(Ahmad Fagam)