in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta tura jami'ai na musamman shiyyar arewa ta tsakiya
2016-07-05 10:24:15 cri
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta tura wasu jami'ai na musamman kimanin 50 zuwa jihar Kogi dake shiyyar arewa ta tsakiyar kasar inda ake fama da tashe tashe hankula.

Jami'in hukumar mai kula da jihar Usman Yakubu, ya shedawa 'yan jaridu a Lokoja cewar, an tura jami'an ne daga Abuja hedkwatar mulkin kasar tun a ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce tawagar jami'an za su gudanar da ayyuka ne da suka hada da farautar maso yin garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami da suka addabi yankunan jihar watanni da dama suka shude.

Yakubu, ya ce tuni aka baza jami'an na musamman zuwa sassan jihar.

A cewarsa, jami'an za su yi aiki tare da takwarorinsu dake jihar, domin kakkabe masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami da sauran masu aikata laifuka wadanda ke cin karensu ba babbaka. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China