Kana bisa kididdigar da tawagar ta yi, an ce, wadanda suka rasa rayukansu a watan Yuli sun hada da fararen hula 844 da kuma jami'an tsaron kasar Iraq 488, kana cikin wadanda suka jikkata, akwai fararen hula 1616, yayin da jami'an tsaron kasar 492.
Tun farkon shekarar 2013, an sha fama da tashe-tashen hankula da kuma hare-haren ta'addanci a kasar Iraq, wandanda suka haddasa babbar illa sosai ga yanayin tsaron kasar, haka kuma, bisa kididdigar da tawagar ba da taimako da MDD ta tura zuwa kasar Iraq ta yi, an ce, a shekarar 2014, aukuwar tashe-tashen hankula da hare-haren ta'addanci a kasar Iraq gaba daya sun haddasa rasuwar fararen hula guda 12.282, yayin da 23.126 suka ji rauni, adadin ya kasance mafi yawa cikin 'yan shekarun nan. (Maryam)