Bisa labarin da 'yan sandan kasar Iraq suka bayar, an ce, masallacin da aka kai hari yana kudu maso yammacin birnin Bagadaza, wani dan kunar bakin wake ya shiga masallacin a yayin da ake gudanar da jana'izar dan kungiyar Hashed al-Shaabi, wanda ya rasu sakamakon yakin da ya yi da kungiyar IS, inda harin da ya haddasa rasuwa da kuma jikkatar mutane 67, sai dai mai yiyuwa ne adadin wadanda suka rasu zai karu sabo da rauni mai tsanani da wadansu suka ji.
Har ila yau a wannan rana , an kai harin boma-bomai ga wani wurin Shiah a garin Sadr dake arewacin Bagadaza, wanda ya haddasa rasuwar mutane guda biyu, yayin 15 suka jikkata.
Ya zuwa yanzu dai, babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin harin, amma wasu na ganin cewa, kungiyar IS na da hannu a harin. Kimanin shekara daya da ta gabata kungiyar shiah ta kasar Iraq ta kafa kungiyar Hashed al-Shaabi domin yaki da kungiyar IS, amma cikin shekarar da ta gabata, kungiyar IS tana ci gaba da samun bunkasuwa, yayin da ta mamaye yankin kasar Iraq da yankin iyakar Syria kimanin kashi daya bisa uku.
A ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba, an kai hare-hare har sau biyu a wani matsugunin jama'a dake birnin Beirut na kasar Lebanon, wadanda suka haddasa rasuwar mutane 37, yayin da sama da 180 suka jikkata, harin da kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kaiwa. (Maryam)