in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Iraqi ya sanar da daukar matakan soji domin 'yantar da birnin Fallujah
2016-05-23 11:12:07 cri
Wasu rahotanni na cewa a yau din nan firaministan kasar Iraqi Haider Al-Abadi, ya sanar da kudurin kasarsa game da daukar matakan soji, don kwace birnin Fallujah daga hannun kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS.

Abadi ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, yana mai cewa sojojin kasar Iraqi, da wasu dakaru masu dauke da makamai da goyon bayan gwamnatinsa ne za su aiwatar da wannan mataki. A jiya Lahadi kuma, sojojin gwamnatin kasar ta Iraqi sun umarci daukacin al'ummun birnin Fallujah da suka fice daga birnin.

Birnin Fallujah dai na lardin Anbar ne wanda ke yammacin kasar Iraqi, yana kuma da nisan kimanin kilomita 69 daga birnin Bagadaza fadar mulkin kasar ta Iraqi. A watan Janairu na shekarar 2014 ne kungiyar IS ta kwace wannan birni daga ikon gwamnatin kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China