in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta yi allawadai da hare-haren ta'addanci a Saudiya
2016-07-08 10:35:31 cri

Gwamnatin Nijar ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis a birnin Niamey, domin yin allawadai da babbar murya kan hare haren da aka kai kan tsarkakkun wuraren addinin musulunci dake Saudiya, lamarin dake nuna rashin imanin ta'addanci ga rayuwar bil adama.

Hare haren kunar bakin wake sun afkawa biranen Djeddah, Qatif da Madina na kasar Saudiya, wadanda suka janyo mutuwar jami'an tsaro da dama, a ranar Litinin da ta gabata, kwanaki biyu na karshen azumin watan Ramadan, da kuma kusantowar sallar Aid el-Fitr.

Gwamnatin Nijar ta nuna goyon bayanta da juyayinta ga hukumomin Saudiya, tana kuma goyon bayan sosai kan matakan da za a dauka a cikin tsarin hukumomin hadin gwiwa, musammun ma kungiyar dangantakar musulunci , domin yaki da ta'addanci daga dukkan fannoni.

Nijar, kasar dake yankin Sahel, na fuskantar barazana tun yau da 'yan shekaru daga dukkan fannoni, musammun ma tare da munanan hare haren kungiyar Boko Haram a yankin kudu maso gabashin kasar mai iyaka da Najeriya, kutsen 'yan ta'adda dauke da makamai dake fitowa daga arewacin makwabciyar Mali, da kuma barazanar yau da kullum ta kungiyoyin 'yan ta'adda da sauran masu fataucin miyagun kwayoyi a bangaren kan iyakarta da kasar Libiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China