in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UEMOA ta zuba kudi kan shirin noma domin tsaron abinci a Nijar
2016-05-27 10:27:18 cri

Kasar Nijar ta samu gajiyar wani tallafin kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) na fiye da Sefa biliyan uku da ya shafi fadin eka 1000 domin bunkasa noma, kiwo da kamun kifi.

Shirin na cikin tsarin shiyya game da sauyin yanayi da kungiyar UEMOA da kasashen mambobin kungiyar suke aiwatarwa a halin yanzu. Manufar shirin ita ce cimma tsaron abinci ga al'ummomi da fuskantar sakamakon sauyin yanayi.

Yarjejeniyar dake da nasaba da shirin ta samu sanya hannun ministan kasa na Nijar dake kula da harkokin noma da kiwo, Albade Abouba, da kuma komishinan dake kula da sashen tsaron abinci na UEMOA, Ibrahima Dieme.

A cewar Albade Abouba, rattaba hannu kan wannan yarjejeniya na gaba- gaban kokarin da hukumomin Nijar suke dauka domin nisantar al'ummomin Nijar daga yunwa, da tattabar musu da yanayin da ya dace wajen samar da albarkatun noma cikin kasa. Kuma shirin zai shafi jihohin Dosso, Maradi, Tahoua da Tillabery. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China