Wata zanga zangar da ya kamata ta gudana a ranar Lahadi bisa jagorancin wasu kungiyoyin fararen hula na kasar Nijar ashirin a karkashin "gungun jan damara domin kare kasa" a dukkan fadin kasar, domin maido da tsarin demokaradiyya, hukumomin kasar sun hana ta bisa wasu dalilai na tsaro.
Makasudin wannan zanga zanga, a cewar masu shiryawa shi ne na yin allawadai da kura kuren da aka samu a lokacin zabukan baya bayan nan a kasar Nijar, wadanda suke sake baiwa shugaba mai ci Mahamadou Issoufou sake lashe zaben shugaban kasa, da kuma hana mulkin danniya a cikin wannan kasa dake yammacin Afrika, a cewarsu.
A birnin Niamey, ana sanar wa kungiyoyin fararen hula duk matakin hana zanga zangar a jajibiri, kuma an jibge jami'an tsaro a muhimman wurare tun safiyar ranar Lahadi. (Maman Ada)