in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta kara wa'adin dokar ta baci na tsawon watanni 3 a yankin Diffa
2016-04-29 09:17:12 cri

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta tsawaita wa'adin dokar ta baci na tsawon watanni 3 a yankin gabashin Diffa wanda zai fara aiki tun daga ranar 28 ga wannan watan na Aprilu, sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro da ake fama da shi a sanadiyyar hare haren mayakan Boko Haram.

Wata majiya daga mahukuntan kasar ta tabbatar da cewa, an dauki wannan mataki na tsawaita wa'adin dokar ta bacin a yankin na Diffa ne, saboda mummunar barazanar da ake fuskanta daga maharan Boko Haram.

A ranar goma ga watan Fabrairun 2015 ne, majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta amince da tsawaita dokar ta bacin, matukar akwai bukatar yin hakan, kamar yadda dokokin tsarin mulkin jamhuriyar Nijar suka tanada.

A lokacin dokar ta bacin, ministan cikin gidan jamhuriyar Najar da gwamnan lardin Diffa suna da ikon ba da umarnin gudanar da bincike a gidajen jama'a a ko wane lokaci.

Tun a watan Fabrairun 2015 ne, yankunan Bosso da Diffa masu makwabtaka da Najeriya suke fuskantar hare hare masu yawa daga mayakan Boko Haram, lamarin da ya haddasa mutuwar daruruwan fararen hula da sojojin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China