Kasar Aljeriya ta yi kira a ranar Litinin ga kasashen Saudiyya da Iran da su nuna sanin ya kamata da sanya wa zukatansu ruwan sanyi domin kaucewa karuwar tashin hankali tsakanin kasashen biyu, dalilin rikicin diplomasiyyar da ya bullo bayan hukumomin Saudiyya sun aiwatar da hukuncin kisa a ranar Asabar kan wani babban malamin Shi'a, Nirm Baqr al-Nirm.
Aljeriya ta yi kira nan take ga manyan jagororin siyasa na kasashen biyu da su sassauta rura wutar gaba domin kaucewa kara tabarbarewar matsalar da ka iya janyo munanan sakamako a fuskar dangantaka da kuma shiyya, a cikin wani yanayi na tsaro mai cike da hadari da ake ciki halin yanzu, in ji sanarwar ma'aikatar harkokin wajen kasar.
A bangaren Aljeriya, ma'aikatar harkokin wajenta ta jaddada fatanta na ganin kada a tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasashe, da kuma ba da kariya yadda ya kamata ga ofishoshin jakadancin kasashe da kananan ofishoshin jakadanci a duk inda suke kuma cikin ko wane hali. (Maman Ada)