A cewar sa, hakan na nuna cewa saurin karuwar yawan makamashin Kwal da aka yi amfani da shi a kasar ya yi kasa zuwa mataki mafi kankanta cikin shekaru 17 da suka wuce. Hakan ya nuna a zahiri, cewa an rage ko kuma canza nau'in makamashin da ake yin amfani da shi a kasar.
A dai wannan rana, yayin wani taro game da makamashi na kasar Sin, Nuer Baikeli ya bayyana cewa, ana kokarin kyautata tsarin makamashi a kasar Sin.
Ya ce an kiyasta cewa, yawan makamashin da aka yi amfani da shi da ba na ma'adinai ba, ya kai kashi 12 cikin dari, adadin da ya karu da kashi 0.8 cikin dari bisa na bara, yayin da yawan makamashin da aka samu daga kwal ya kai kashi 64.4 cikin dari, adadin da shi ma ya ragu da kashi 1.7 cikin dari. (Fatima)