Sin za ta samar da damar zuba jari na dallar Amurka biliyan dari 25 a fannin sabbin makamashi domin fuskantar matsalar sauyin yanayi
A yau ne yayin taron koli kan sauyin yanayi na kasar Sin da reshen kasar Sin na kungiyar kula da manufofin inganta rayuwar al'umma ta MDD UNGC ta kira, mai ba da shawara ga magatakardan MDD Ban Ki-moon kan harkokin sauyin yanayi Rae Kwon Chung ya bayyana cewa, bisa burin da kasar Sin ta tsara kan fuskantar sauyin yanayi na shekarar 2030, kasar za ta samar da gurabun zuba jari da ya kai dallar Amurka biliyan 2500 a fannin sabbin makamashi domin fuskantar matsalar sauyin yanayi, matakain da zai taimaka wajen sa kaimi ga kamfanonin kasar su shiga a dama da su a kokarin da ake na magance matsalar sauyin yanayi cikin himma da kwazo.
Shi ma mataimakin babban sakataren kungiyar UNGC Georg Kell ya ce, ya zuwa karshen shekarar 2016, da alamun kasar Sin za ta kasance kasuwar kwal mafi girma a duniya. (Maryam)