in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga Afrika da ta yi koyi da Sin wajen bunkasa makamashin da ake iya sake amfani da shi
2016-05-26 10:30:56 cri

Wani kwararre game da muhallin kasa da kasa ya yi kira a ranar Laraba ga kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara da su yi amfani da gajiyar kwarewar Sin ta fuskar bunkasa makamashin da ake iya sake amfani da shi.

David Rodgers, kwararre game da yanayi a asusun muhallin duniya (GEF) ya bayyana cewa, kasar Sin na amfani da sabbin fasahohin samun makamashi na iska da hasken rana, da a lokacin baya aka daukar su na masu hannu da shuni.

Matakin Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen kasancewa jagora a duniya a fannin samar da makamashi ga al'ummomi a cikin farashi mai rahusa, in ji mista Rodgers a yayin babban taron MDD kan muhalli (ANUE)

Bayan bullo da wani shirin bunkasa sabbin makamashi bisa tsawon shekaru biyar a shekarar 2014, Sin ta kara zuba jarinta a cikin sabbin makamashi da kashi 17 cikin 100, zuwa dalar Amurka biliyan 102,9.

Wajibi ne Afrika ta fitar da manufofi masu karfi wajen amfani da makamashin hasken rana da iska, ganin cewa wannan nahiya har yanzu tana fama da karancin makamashi, in ji mista Rodgers. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China