Bankin ci gaban kasashen Afrika na ADB, na daukar hakar albarkatun makamashi na Afrika a matsayin daya daga cikin muhimman ayyuka, in ji shugaban bankin, Akinwumi Adesina a ranar Laraba a albarkacin "makon makamashi" da aka shirya a ranakun 14 zuwa 18 ga watan Satumba a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire. Makon da bankin ADB ya shirya tare da abokan huldarsa na da manufar yin nazari kan ci gaban wannan bangare na makamashi a Afrika, da kuma baiwa wannan babban arziki darajarsa a nahiyar.
Haka kuma, makon ya mai da hankali kan batun haskaka wurare da samar wutar lantarki a Afrika.
Bayan an zabe shi a matsayin shugaban bankin ADB a ranar 1 ga watan Satumba, mista Adesina ya jaddada niyyar hukumarsa ta sanya makamashi daga cikin muhimman batutuwan dake gabansa.
Afrika tana arzikin makamashin da ba ya da iyaka a fannin hasken rana, iska, ruwa da kuma zafin karkashin kasa, in ji shugaban bankin ADB.
Bude albarkatun makamashi na Afrika mai tarin yawa, domin Afrika, zai kasance daya daga cikin manyan ayyukan bankin ADB, in ji mista Adesina tare da cewa, bankin kasashen na Afrika zai kasance babbar jagora a wannan muhimmin aiki.
Mista Adesina ya bayyana cewa, bankin ADB zai kaddamar tare da shawarwarin da aka tsai da a Abidjan, da wata sabuwar jarjejeniyar makamashi domin Afrika, wadda za ta kai ga cimma gaggauta samar da wutar lantarki a nahiyar Afrika baki daya. (Maman Ada)